logo

HAUSA

Ana nazarin lokaci da wurin da za a gudanar da sabon zagayen tattaunawar nukiliyar Iran

2022-07-04 10:50:07 CMG Hausa

Babban mai shiga tsakani game da nukiliyar Iran Ali Bagheri Kani ya ce ana nazarin lokaci da wurin gudanar da sabon zagayen tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.

Kamfanin dilancin labarai na IRNA na kasar ya ruwaito Bagheri Kani na cewa, tattaunawar Doha, ta gudana bisa yadda aka tsara, yana mai cewa, Iran da Tarayyar Turai na nazarin lokaci da wurin da za a gudanar da tattaunawa ta gaba.

Sai dai, bai fayyace ko tattaunawar za ta kasance tsakanin Iran da kasashen dake cikin yarjejeniyar wato Birtaniya da Sin da Faransa da Rasha da Jamus ba, ko kuma za ta gudana ne ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka.

Iran da Amurka sun gudanar da wata tattaunawa da ba ta kai tsaye ba a ranekun Talata da Laraba a Doha, babban birnin Qatar, inda Enrique Mora, jami’in Tarayyar Turai, ya kasance mai shiga tsakani, da nufin shawo kan sabanin dake tsakaninsu game da farfado da yarjejeniyar. (Fa’iza Mustapha)