logo

HAUSA

Rundunar ’yan sandan Najeriya za ta binciki zargin garkuwa da mutane a wata coci

2022-07-04 12:33:53 CMG Hausa

Rundunar ’yan sandan Najeriya reshen jihar Ondo dake kudu maso yammacin kasar, ta ce zata gudanar da cikakken bincike game da zargin garkuwa da wasu mutane, galibin su yara kanana su 77 a wata coci.

Kakakin rundunar Funmilayo Odunlami, ya shaidawa manema labarai hakan a jiya Lahadi, a birnin Akure fadar mulkin jihar ta Ondo, inda ya ce ’yan sanda sun ceto mutanen 77 a daren ranar Juma’a, bayan samun wasu bayanan sirri. Ya ce jami’an ’yan sanda sun gano mutanen ne a wani wuri da aka boye su dake kasan ginin cocin.

Odunlami ya kara da cewa, binciken farko-farko da aka yi ya nuna cewa, limamin cocin ne ya yaudari mutanen, da wani alkawarin bogi mai nasaba da addini, inda ya nuna musu cewa, shi kadai ya wajaba su yiwa biyayya, sabanin iyayen da suka haife su. Kaza lika kakakin na ’yan sanda ya ce za su fitar da cikakken bayani bayan kammala bincike. (Saminu Hassan)