logo

HAUSA

Shugaban Guinea Bissau ya dare shugabancin ECOWAS

2022-07-04 10:05:13 CMG Hausa

A wani ci gaban kuma, an zabi shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Mokhtar Sissoco Embalo, a matsayin sabon jagoran kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma, wato ECOWAS a takaice na karba-karba.

An zabi shugaba Embalo ne a jiya Lahadi, yayin taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS, inda zai maye gurbin shugaban kungiyar mai barin gado, kuma shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, wanda ke rike da wannan mukami tun daga watan Satumbar shekarar 2020.

An dai zabi shugaba Embalo ne ba hamayya, kuma cikin jawabinsa na amincewa, shugaban na Guinea Bissau ya alkawarta yin aiki tukuru, a fannin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin yammacin Afirka.

Ya ce "Duk da tarin kalubale da ake fuskanta sakamakon ayyukan ’yan ta’adda, da sauran matsalolin da duniya ke fama da su, na yi imanin cewa, hadin kan ECOWAS zai ba da damar magance su".  (Saminu)