logo

HAUSA

Babbar editar Nature: Bai kamata a shigar da siyasa a hadin gwiwar kimiyya ba

2022-07-03 16:41:50 CMG Hausa

 

Magdalena Skipper, babbar editar mujallar Nature, ta kasar Birtaniya, ta bayyana a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, dole ne a taimakawa kimiyya a tsakanin kasa da kasa, kuma bai kamata a shigar da siyasa cikin hadin gwiwar kimiyyar ba.

Da take buga misali game da batun baki biyun da ake yawan samu daga wasu yankunan Turai da Amurka a shekarun baya-bayan nan, Skipper ta yi tsokaci cewa, “abin bakin ciki ne”, kuma “abin damuwa ne,” sannan  ta ce, idan lamarin ya ci gaba da faruwa, kowa zai iya yin hasara, kuma wadanda za su samu hakikanin nasara su ne wadanda suka yi aiki tukuru wajen wanzar da hadin kai da yin musaya.

Dr. Skipper, ta bukaci goyon bayan gudanar da bincike na kasa da kasa bisa hadin gwiwa, tana mai cewa, “dukkan wasu tambayoyi masu sarkakiya da ake fuskanta, sun shafi kasa da kasa ne, kuma tilas ne a samar da amsoshinsu a matsayin wani bangare na hadin gwiwar kasa da kasa".

Hadin gwiwar binciken kimiyyar kasa da kasa yana kasancewa a matsayin wata gadar musayar bayanai a tarihi, ko da kuwa a lokutan da ake fuskantar wahalhalu ne, kamar yadda mujallar ta Nature ta lura da hakan. Yin cudanya da juna, maimakon nuna wariya, shi ne hanyar da za ta samar da zaman lafiya, da aza harsashin tubalin gina wata gadar cudanyar al’adu, da kyautata tuntubar juna, a tsakanin al’ummun duniya.(Ahmad)