logo

HAUSA

Masani: Amurka Take Yada Karairayin Aikin Tilas Don Bata Sunan Kasar Sin

2022-07-03 17:52:29 CMG Hausa

Wani kwararren Ba-Amurke ya ce, “Ni a ra’ayi na, batun dokar aikin tilas ta Uyghur, ba komai ba ne illa makircin siyasa da aka kirkira domin bata sunan kasar Sin.

Daniel Kovalik, wani lauyan kasar Amurka dake koyar da hakkin dan Adam na kasa da kasa a kwalejin nazarin dokoki na jami’ar Pittsburgh, ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, "Hakika dai, wannan ba batu ne da ya shafi hakkin dan Adam ba, tabbas. Sai dai kawai, batu ne da ya shafi yunkurin gwamnatin kasar Amurka na neman shafawa kasar Sin bakin fenti da zubar mata da kima.”

Kasar Amurka tana amfani da batun hakkin dan Adam a matsayin wani salon makirci domin yakar dukkan wadanda take son lalata hulda da su a cewar Kovalik. Ya ce, lamarin ba shi da wata alaka da batun hakkin dan Adam, kawai dai batu ne da ya shafi moriyar Amurka ta fannonin tattalin arziki da manyan tsare-tsare.

A cewar masanin, babu abin da ya shafe su da hakkin dan Adam na kasar Sin, abin da kawai ya dame su shi ne, kasar Sin ta zama wata babbar mai fada-a-ji ta fannin tattalin arziki a duniya, kuma mai karfi ta fuskar diflomasiyya. Kana suna yunkurin fakewa da batun hakkin dan Adam ne wajen lahanta kasar Sin kasancewar suna daukar Sin a matsayin babbar abokiyar takarar tattalin arziki.

Kovalik ya kara da cewa, “Ina tsammanin abin da kawai ya fi dacewa shi ne kasar Sin ta ci gaba da abubuwan da take yi, ta kara matsawa gaba, ta ci gaba da ayyukan gina hanyoyin mota, da jiragen kasa, ta ci gaba da ayyukan samar da dawwamamman ci gaba, da tsame mutane daga kangin talauci."

Ya ci gaba da cewa, kamata ya yi Sin ta ci gaba da abubuwan da ta sanya a gabanta. Duniya tana kallon yadda kasar Sin take. Batun yada farfagandar kasashen yammacin duniya ba zai taba sanyaya gwiwar kasar Sin kan manufofinta ba.(Ahmad)