logo

HAUSA

An kammala taron MDD kan teku, inda aka amince da Yarjejeniyar Lisbon

2022-07-02 17:50:37 CMG Hausa

Sama da kasashe 150 ne suka amince tare da cimma Yarjejeniyar Lisbon, dake da nufin inganta daukar dabaru bisa kimiyya da kirkire kirkire domin magance batutuwa na gaggawa da suka shafi teku, a karshen taron MDD game da batun, wanda aka kammala jiya Juma’a.

Kasashen sun amince da daukar matakai kamar na karfafa tattara bayanai da bayar da dama ga rawar da mutanen asali na yankuna ke takawa, wajen yayata dabarun rage fitar da hayaki mai guba daga ababen sufuri na ruwa, musamman jiragen ruwa.

Kasashen sun kuma amince da inganta hanyoyin samar da kudi domin cimma tattalin arziki mai dorewa a bangaren teku da karfafawa mata da kananan kabilu gwiwar shiga ana damawa da su a harkokin da suka shafi tattalin arzikin bangaren. (Fa'iza Mustapha)