logo

HAUSA

Tashoshin radio da talabijin na CGTN sun fara watsa shirye-shirye a yankin Hong Kong

2022-07-02 17:47:21 CMG Hausa

Yayin da ake bukukuwan cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, kafar talabijin ta Documentary da tashar rediyo ta The Greater Bay, na kafar yada labarai ta CGTN ta kasar Sin, sun fara watsa shirye-shiryensu a yankin.

Tashar rediyo ta The Greater Bay, ta watsa bukukuwan murnar kai tsaye, cikin harshen Cantonese na yankin, daga cibiyar taruka da nune-nune ta Hong Kong, ciki har da na kaddamar da sabuwar gwamnatin yankin.

Shirye-shirye da dama masu kayatarwa da aka gabatar kan maudu’ai daban-daban da aka watsa a ranar farko, sun ja hankalin mazauna yankin, inda kuma bangarori daban-daban daga Hong Kong din da Macao, suka yi ta aikewa da sakon taya tashoshin murna. (Fa’iza Msutapha)