logo

HAUSA

Harkokin ciniki tsakanin babban yankin Sin da Hong Kong ya ninka fiye da sau 6

2022-07-01 10:25:26 CMG HAUSA

 

A bana ne, yankin Hong Kong ke cika shekaru 25 da dawowa karkashin ikon kasar Sin. A cikin shekaru 25 da suka gabata, yawan ciniki tsakanin babban yankin Sin da yankin musamman na Hong Kong, ya ninka sau 6.1. Ya zuwa karshen shekarar 2021 kuwa, babban yanki ya samu jarin da darajarsa ta kai fiye da dalar Amurka tiriliyan 1.4 daga yankin Hong Kong, wanda ya kai kashi 57.6 cikin 100 na adadin jarin da kasashen ketare suka zuba. Wannan na nuna cewa, yankin Hong Kong ya kara taka rawa a matsayin muhimmiyar kafa ta harkokin kasuwanci da zuba jari.

Filin jirgin sama na kasa da kasa na Hong Kong, da gadar dake hade yankin Hong Kong da birnin Zhuhai da yankin Macao, da hanyar jirgin kasa mai saurin tafiya tsakanin Guangzhou zuwa Shenzhen zuwa Hong Kong, wasu daga cikin jerin "manyan ayyuka", sun kara kusanto yankin Hong Kong da babban yanki, tare da inganta mu'amalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarorin biyu.

A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, gwamnatin tsakiya ta nuna goyon baya sosai kan shigar yankin Hong Kong cikin hadin gwiwar gina “shawarar ziri daya da hanya daya” da kuma shigar yankin cikin yanayin ci gaban kasa baki daya. Tun daga shekarar 2013, kamfanonin Hong Kong da na babban yanki, sun hada hannu don gudanar da shawarwarin zuba jari a kasashen da suka amince da shawarar ziri daya da hanya daya" tsawon shekaru bakwai a jere, inda suka jawo hankulan sama da kamfanoni cikin gida 1000 domin shiga a dama da su, tare da yayata aniyyar hadin gwiwar zuba jari sama da 70. (Ibrahim Yaya)