logo

HAUSA

Shugaba Xi ya yaba da ci gaban kirkire-kirkire da fasahar Hong Kong

2022-07-01 10:12:47 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, bisa tallafin gwamnatin tsakiya, yankin Hong Kong ya yi amfani da fifikonsa, wajen samun nasarori masu ma'ana a fannin muhimman bincike, da hazaka, da kuma ci gaba a fannin kirkire-kirkire da fasaha a shekarun baya-bayan nan.

Xi ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, a yayin ziyarar duba rukunin masana’antun kimiyya na Hong Kong, bisa rakiyar jagorar yankin musamman na Hong Kong Carrie Lam.

Shugaba Xi ya ce, kamata ya yi gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ta ba da cikakken muhimmanci kan rawar da sabbin fasahohi ke takawa, wajen ba da taimako da jagoranci ga ci gaban tattalin arziki.

Yayin da yake zantawa da masana ilimi, da masu bincike, da wakilan matasa na masana'antun kirkire-kirkire, Xi ya yi kira ga yankin Hong Kong, da ya kara yin hadin gwiwa da biranen dake babban yanki cikin babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao, da karfafa hadin gwiwar ci gaban kamfanoni, da jami'o'i, da cibiyoyin bincike, da kara zage damtse don daga matsayin yankin Guangdong-Hong Kong-Macao, zuwa wata cibiyar kimiya da fasahar kirkire-kirkire ta duniya.

Xi ya bayyana fatan cewa, za a ci gaba da raya al'adun kaunar kasa da Hong Kong, tare da ba da gudummawa sosai, don gina kasar Sin wajen zama jagorar kimiyya da fasaha ta duniya. (Ibrahim)