logo

HAUSA

Ma’aikatar wajen kasar Sin ta musanta kalaman Amurka da Birtaniya game da yankin Hong Kong

2022-07-01 20:48:53 CMG Hausa

Wasu rahotanni na cewa, Amurka da Birtaniya, da dai sauran wasu kasashen yamma, sun fitar da sanarwar da ma kalamai mabanbanta, a dab da ranar bikin murnar cikar yankin Hong Kong shekaru 25 da komawa karkashin ikon kasar Sin.

Cikin irin wadancan kalamai dai, kasashen na yamma sun rika cewa, wai an lalata dimokaradiyya da tsarin bin doka, da ‘yancin al’umma a Hong Kong. Kaza lika wai a cewar su, kasar Sin ta gaza cika alkawarin ta na aiwatar da manufar nan ta "Kasa daya amma tsarin mulki biyu ".

Game da wadannan zarge zarge, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce wadannan kasashe ba su cancanci furta kalaman batanci kan Hong Kong mai bunkasuwa da daidaito ba.

Zhao Lijian, wanda ya yi wannan tsokaci a yayin taron manema labarai na Juma’ar nan, ya kara da cewa, shugaban kasar Sin ya gabatar da muhimmin jawabi, a bikin cikar yankin Hong Kong shekaru 25 da komawa karkashin kasar Sin, ya kuma jaddada manyan nasarorin da aka cimma, a fannin aiwatar da manufar nan ta "Kasa daya amma tsarin mulki biyu " cikin shekarun 25 da suka gabata, kuma ya yi nuni da cewa, a bayyane take, manufar "Kasa daya amma tsarin mulki biyu" tana da inganci, an kuma gwada nagartar hakan a zahiri, manufar ta kuma dace da babbar moriyar kasar Sin baki daya, da moriyar yankunan Hong Kong da Macao, ta kuma samu cikakken goyon bayan sama da al’ummar Sinawa biliyan 1.4, da al’ummun dake zaune a yankunan HK da Macao, baya ga amincewa da ta samu daga sassan kasa da kasa. Har ila yau, gwamnatin tsakiyar kasar Sin, za ta ci gaba da aiwatar da manufar "Kasa daya amma tsarin mulki biyu" cikin tsawon lokaci, kuma ba za ta taba sauya matsayar ta a kan hakan ba. (Saminu)