logo

HAUSA

Shugaba Xi ya duba rundunar PLA dake Hong Kong

2022-07-01 22:56:37 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya duba yanayin rundunar‘yantar da jama’ar kasar Sin ko PLA a takaice wadda ke yankin musamman na Hong Kong, a Juma’ar nan.

Yayin rangadin rundunar, Xi Jinping, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar, ya mika sahihiyar gaisuwa ga daukacin jami’an rundunar ta Hong Kong.

Shugaba Xi ya isa Hong Kong ne a jiya Alhamis, domin halartar bikin cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, da kuma bikin rantsar da hukumar gudanarwar yankin na Hong Kong ta 6. (Saminu)