logo

HAUSA

Xi Jinping ya baro Hong Kong bayan nasarar kammala ayyuka daban-daban a Hong Kong

2022-07-01 16:21:39 CMG Hausa

Xi Jinping, babban sataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasa, kana shugaban babbar hukumar sojojin kasar Sin, ya kammala ayyuka a rangadinsa a yankin Hong Kong na kasar Sin, kuma ya baro yankin a cikin wani jirgin kasa na musamman da tsakar ranar 1 ga watan Yuli.

A tashar jirgin kasa mai saurin tafiya ta West Kowloon, wakilai daga dukkan fannonin rayuwa na Hong Kong da kananan yara sun yi ta kada tutar kasa, da tutar yanki na musamman na Hong Kong, tare da mika furanni don nuna fatan alheri. Shugaba Xi Jinping da mai dakinsa Peng Liyuan, sun daga hannu domin yin bankwana da al’ummar yankin.(Ahmad)