logo

HAUSA

Xi Jinping: “kasa daya amma tsarin mulki iri biyu” mataki mai kyau na raya yankin Hong Kong

2022-06-30 11:59:37 CMG HAUSA

 

Bayan dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin yau shekaru 25 da suka gabata, yankin ya samu ci gaban a zo a gani. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi hangen nesa matuka kan bunkasuwar yankin don tabbatar da cewa, an samu ci gaba mai dorewa karkashin manufar “kasa daya amma tsarin mulki iri biyu”. Xi Jinping ya ce, “Tun bayan dawowar yankunan Hong Kong da Macao karkashin ikon kasar Sin, wannan manufa ta samu amincewa daga bangarori daban-daban. Abin da ya shaida cewa, ita ce hanya mafi dacewa wajen warware matsalolin da aka bari yankunan biyu, kuma manufa ce mai kyau wajen raya yankunan biyu mai dorewa a cikin dogon lokaci.”

Bisa goyon bayan kwamitin tsakiyar jam’iyyar JKS karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, jerin tsare-tsare sun baiwa yankin Hong Kong zarafi da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba. Daga shawarar “ziri daya da hanya daya” da tsarin raya babban yankin Guangdong da Hong Kong da Macao da kuma baiwa yankin taimamako wajen yakar cutar COVID-19 kuma tsarin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 ya baiwa yankin sabon matsayi. Duk wadannan sun shaida cewa, ci gaban da aka samu karkashin wannan manufa, ta samu amincewa daga bangarori daban-daban, kazalika yankin na hanzarta shiga tsarin gudanar da harkokin kasa, abin da zai tabbatar da bunkasuwar babban yanki da kuma taimakawa juna bisa fifikonsu. (Amina Xu)