logo

HAUSA

Sin ta yi watsi da kalaman sakatariyar wajen Birtaniya game da batun Taiwan

2022-06-30 21:28:03 CMG Hausa

A yau Alhamis ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi watsi da kalaman sakatariyar wajen kasar Birtaniya Liz Truss, wadda aka jiyo ta na cewa wai, “Akwai hadari karara idan har kasar Sin ta rungumi gurguwar fahimta, wadda ka iya haifar da mamaye yankin Taiwan".

Zhao ya ce ko shakka ba bu, batun yankin Taiwan harka ce ta cikin gidan kasar Sin, kuma ba bu wani bangare na daban, da ya dace ya tsoma hannu cikin batun. Wannan ita ce ka’idar kasa da kasa da ta dace a bi.

Jami’in ya kara da cewa, Sin na nacewa ka’idar dunkulewar sassan ta bisa lumana, da tsarin “Kasa daya amma tsarin mulki biyu", kuma za ta yi dukkanin mai yiwuwa, wajen tabbatar da hade sassan yankunan ta cikin lumana. A daya hannun kuma, ba za ta zuba ido ta bari ‘yan awaren yankin Taiwan su ci karen su ba babbaka ba.  (Saminu)