logo

HAUSA

Ministan wajen Sin: Kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da mambobin SCO wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma

2022-06-30 10:39:14 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashe mambobin kungiyar kawancen Shanghai ko kuma (SCO) a takaice, domin aiwatar da “ruhin Shanghai" da kuma kokarin gina al’umma mai kyakkyawar makoma.

Wang Yi ya yi wannan tsokaci ne a yayin da ya jagoranci taron tattaunawa ta kafar bidiyo tare da kasashe takwas na mambobin kungiyar SCO, wanda ya kasance a matsayin bikin tunawa da cika shekaru 20 da kafa yarjejeniyar kungiyar, da kuma bikin murnar sanya hannu kan yarjejeniyar kungiyar karo na 15, wanda ya shafi kulla yarjejeniyar dogon lokaci ta kyautata makwabtaka, da abokantaka, da kuma hadin gwiwa a tsakanin mambobi kasashen.

Ya ce yarjejeniyar ta fayyace manufofi da muhimman ayyukan dake shafar batun daga matsayin aikin wanzar da zaman lafiya da ci gaban shiyyar, da kafa muhimman manufofin amincewar juna, da cin moriyar juna, da tuntubar juna, gami da amincewa da kungiyar a matsayin ta kasa da kasa a hukumance da nufin samar da wani sabon tsarin ci gaba mai matukar karfi. (Ahmad)