logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da jawabi a yayin bikin maraba da zuwansa a tashar jiragen kasa ta Hong Kong West Kowloon

2022-06-30 16:54:39 CMG Hausa

Da yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a yayin bikin maraba da zuwa da aka shirya masa a tashar jiragen kasa mai saurin gaske ta Hong Kong West Kowloon.

Xi Jinping ya isa Hong Kong na kasar Sin ne, ta jirgin kasa mai saurin gaske, don halartar bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong kasar Sin da kuma bikin rantsar da gwamnati ta shida ta yankin musamman na Hong Kong da za a yi a ranar 1 ga watan Yuli, da kuma yin rangadi a yankin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)