logo

HAUSA

Xi Jinping: Muddin muka tsaya tsayin daka kan "kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu", ko shakka babu makomar Hong Kong za ta yi kyau

2022-06-30 19:48:04 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ne, ta jirgin kasa mai saurin gaske da yammacin yau Alhamis, don halartar bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong kasar Sin, da kuma bikin rantsar da gwamnati ta shida ta yankin, wanda za a gudanar a ranar 7 ga watan Yuli, kana zai yi rangadi a yankin.

A tashar jiragen kasa mai saurin gaske ta Hong Kong West Kowloon, jama'a daga sassa daban-daban na Hong Kong sun yi wa Xi Jinping maraba sosai. A jawabin da ya yi a bikin maraba da zuwa, Xi Jinping ya bayyana cewa, ranar 1 ga watan Yuli na bana, ake bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong kasar Sin, kuma al’ummar kasar Sin na kabilu daban daban za su yi murnar bikin tare da ‘yan uwa na Hong Kong.

Xi Jinping ya kuma taya murna, da nuna fatan alheri ga 'yan uwa na Hong Kong. Ya ce,

"Shekaru 5 ke nan da ziyara ta da ta gabata a Hong Kong. A cikin shekarun 5 da suka gabata, ina ta mai da hankali kan Hong Kong, zuciyata, da zuciyar gwamnatin tsakiya suna tare da ’yan uwan Hong Kong.”

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a cikin lokutan da suka gabata, yankin Hong Kong ya jure wa jarrabawa masu tsanani sau da yawa, tare da shawo kan ko wane hadari da kalubale. Daga bisani, Hong Kong ya sake farfadowa bayan durkushewa, a yanzu kuma yana kuma nuna kuzari mai karfi. 

“Hakikanin abubuwa sun shaida cewa, 'kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu' na da karfi sosai, tsari ne da zai iya tabbatar da samun wadata da zaman karko mai dorewa a Hong Kong, da kuma kiyaye alheri da moriyar 'yan uwa na Hong Kong. Kamar yadda a kan ce ‘Idan mun dage tafiya, za mu isa wurin da muke so’. Muddin muka tsaya tsayin daka kan manufar "kasa daya, amma tsarin mulki iri biyu", ko shakka babu makomar Hong Kong za ta yi kyau, kuma tabbas Hong Kong zai ba da babbar gudummawa wajen farfado da al'ummar kasar Sin!” (Mai fassara: Bilkisu Xin)