logo

HAUSA

Xi Jinping ya kai rangadi birnin Wuhan

2022-06-29 19:58:49 CMG Hausa

hugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada aniyar kasarsa na cigaba da tallafawa fannin kimiyya da fasaha, bisa ikon da kasar ke da shi na kashin kan ta, tare da bayyana aniyar kasar Sin na kara bunkasa cigaban kasa ta hanyar dogaro da kanta, da tsayawa da kafafunta, da kuma kiyaye tsaron ci gaban kasar.

Xi, ya yi wannan tsokaci ne a jiya Talata, a lokacin da ya kai ziyarar aiki birnin Wuhan, fadar mulkin lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin.

a yake tsokaci game da yaki da annobar COVID-19, shugaba Xi ya ce matakan da kasar sa ke aiwatarwa, sun yi matukar kare rayuka da lafiyar al’umma. Ya ce duba da yawan jama’ar ta, idan da Sin ta bi salon barin jikin al'umma ya samar da kariya da kansa bayan harbuwar kaso mai yawa na al'aumma, ko ta bar yanayi yayi halin sa, da kasar ta fuskanci mummunan bala’ai.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, manufar Sin ta tabbatar da dakile dukkanin cutar a duk inda ta bulla, tsari ne na kwamitin kolin JKS, wanda ya dace da yanayi da akidun jam’iyyar, da ma halayen da kasar ke ciki.

Xi ya ce "Ko da ma matakan da ake dauka na da wasu tasiri na gajeren lokaci a fannin tattalin arziki, ba za mu sanya rayuka da lafiyar jama’a cikin hadari ba, dole ne mu kare al’umma, musamman ma tsofaffi da yara kanana”.

Daga nan sai shugaban na Sin ya sha alwashin ci gaba da ingiza fannonin tattalin arziki, yana mai kira ga kwamitocin jam’iyya, da sassan gwamnatoci a dukkanin matakai, da su yi aiki tukuru wajen shawo kan wahalhalun da jama’a ke fuskanta, da ma tasirin da matakan ke yi ga tattalin arziki, da rayuwa da ayyukan al’umma. (Saminu)