logo

HAUSA

An yaba ingancin babbar hanyar mota da kamfanin kasar Sin ta shimfida a kasar Aljeriya

2022-06-29 09:44:17 CMG Hausa

            

Babban darektan hukumar kula da manyan tituna ta kasar Aljeriya Mohamed Khaldi ya yaba da ingancin aikin babbar hanyar mota da wani kamfanin kasar Sin ta shimfida a kasar, da kuma gudummawar da kamfanin yake bayarwa wajen raya zamantakewa da tattalin arzikin mazauna yankin.

Babban darektan ya bayyana cewa, hanyar mai tsawon kilomita 53 da kamfanin gine-gine na kasar Sin CSCEC ya aiwatar, ya saukaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki yadda ya kamata, da rage kudin sufuri, da kuma inganta harkokin tafiye-tafiye na mazauna yankin.

Khaldi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da mambobin kwamitin tuntubar juna a kan babbar hanyar Sahara, yayin rangadin wani kaso na mashigar hanyar da ta wuce zuwa yankin Sahara mai tsawon kilomita 53, aikin da ya shafi nahiyar da ya hada kasashen Afirka shida, wato Aljeriya, da Chadi, da Mali, da Nijar, da Najeriya, da kasar Tunisiya.

Baya ga karin jimillar tsawon sama da kilomita 9,000, babbar hanyar ta kunshi sashin Algiers-Lagos, wanda ke da tsawon kusan kilomita 4,500.

Domin gina sashen, kamfanin CSCEC ya samar da ayyukan yi sama da 10,000 a Aljeriya tare da horar da kwararru sama da 2,000 a fannin gine-gine, kamar yadda alkaluman da kamfanin ya fitar suka nuna.  (Ibrahim)