logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijer ya gana da mataimakiyar magajin garin birnin Yamai

2022-06-29 10:07:23 CMG Hausa

A jiya ne, jakadan Sin dake jamhuriyar Nijer Jiang Feng ya gana da Madam Bakary, mataimakiyar magajin garin birnin Yamai, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan karfafa mu’amular abokantaka.

Madam Bakary ta bayyana cewa, har yanzu, wasu dalibai dake birnin Yamai suna karatu a azuzuwan ciyayi. A baya an sha samun tashin gobara a wasu azuzuwan ciyayi, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi mai tarin yawa. Don kyautata yanayin karatu da bunkasa sha’anin bada ilmi a kasar Nijer, kasar ta tsara shirin gaggawa na kawar da azuzuwan ciyayi. Ta ce, kasashen Nijar da Sin na da zumunci mai zurfi a tsakaninsu, tana kuma nuna godiya ga kasar Sin kan goyon baya da take baiwa Nijiar wajen raya birnin Yamai, kana Nijer tana fatan Sin za ta goyi bayan shirin kawar da azuzuwan ciyayi a kasar.

A nasa bangare, jakada Jiang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Nijer ta maida hankali ga sha’anin bada ilmi, kuma shirin kawar da azuzuwan ciyayi da gwamnatin ta kaddamar, zai taimakawa karin yaran samun ilimi, a yanayi mai inganci da tsaro. Sin da Nijer ’yan uwa ne, kuma kasar Sin tana taimakawa kasar Nijer a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Haka kuma Sin tana maida hankali kan damuwar gwamnatin kasar Nijer kan sha’anin bada ilmi, don haka, tana son samar da gudummawa ga wannan shiri gwargwadon karfinta. (Zainab)