logo

HAUSA

Rasha ta halatta shigo da kayayyaki marasa iznin mallakar fasaha yayin da kasashen yamma suka kakaba mata takunkumi

2022-06-29 14:47:08 CMG Hausa

 

   

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata doka, da ta halatta shigo da kayayyaki da ba su da yancin mallakar fasaha a kasar, a wani yunkuri na daidaita farashin kayayyaki, a gabar da kasar ke fama da takunkuman tattalin arziki da kasashen yammacin duniya suka kakaba mata.

Ita dai wannan doka ta ba da kariya ga kamfanonin kasar Rasha, wadanda ke shigo da wasu nau'ikan kayayyaki ba tare da izinin masu mallakar fasaha ba, abin da ake kira shigo da kayayyakin da ba su da yancin mallakar fasaha, daga yiwuwar fuskantar biyan tara, gudanarwa da aikata laifuka.

A cewar shugaban majalisar dokokin kasar Rasha ta Duma, Vyacheslav Volodin, manufar halatta shigo da irin wadannan kayayyaki, ita ce kare tattalin arzikin Rasha da ma 'yan kasar, daga takunkuman tattalin arzikin da aka sanyawa kasar, da saukaka kasuwancin kayayyakin da suka dace da daidaita farashinsu. (Ibrahim Yaya)