logo

HAUSA

MDD ta nuna bakin ciki kan gawarwakin bakin hauren da aka gano samun mutu a jihar Texas ta Amurka

2022-06-29 10:17:54 CMG Hausa

Ofishin yada labarai na babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana a jiya Talata cewa, "Mun yi matukar bakin ciki" da labarin da muka samu cewa, 'yan ci-rani da dama sun mutu a cikin wata tirela da aka yi watsi da ita a San Antonio a jihar Texas ta Amurka.

Wata sanarwa da ofishin ya rabawa manema labarai ta bayyana cewa, dole ne hukumomi a Amurka da Mexico su yi bincike tare da gurfanar da duk wadanda ke da hannu a cikin jerin abubuwan da suka haifar da wannan bala'i.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, Stephane Dujarric, mai magana da yawun magatakardan MDD, ya jaddada bukatar dukkan bangarori da su hada kai, don daukar kwararan matakai na taimakawa wajen hana irin wannan mace-mace a tsakanin mutanen da ke bulaguro.

Hukumomin yankin sun sanar da cewa, adadin bakin hauren da suka mutu a San Antonio da aka gano ya karu zuwa 50. (Ibrahim Yaya)