logo

HAUSA

Sin: Ya wajaba G7 ta kauracewa tsoma baki cikin harkokin gidan Sin

2022-06-29 21:53:05 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ja hankalin kungiyar G7, da ta kauracewa bata sunan kasar Sin, da ma tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida ta dukkanin hanyoyi.

Zhao ya yi wannan tsokaci ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. Hakan na zuwa ne bayan da a jiya Talata, mambobin kungiyar ta G7 suka fitar da sanarwar bayan taron su, wadda a cikin ta suka ambaci sunan kasar Sin har sau 14, suna nuna yatsa game da harkoki a yankin Hong Kong, da jihar Xinjiang, da batun hakkin bil adama da sauransu. (Saminu)