logo

HAUSA

Yankin Hong Kong ya kiyaye matsayinsa na cibiyar hada-hadar kudi ta duniya

2022-06-29 14:02:52 CMG Hausa

Alkalum kididdigar da aka fitar sun nuna cewa, tun daga shekarar 1998 zuwa yanzu, GDP na yankin Hong Kong na kasar Sin, ya ninka sau biyu, wato ya kai dalar Hong Kong triliyan 2.8 ko fiye. Yawan cinikin kaya a yankin ya karu da ninki fiye da biyu, wato ya kai dalar Hong Kong triliyan 10, wanda ya kai matsayi na shida a duniya. Yawan mutanen da suka samu aikin yi, ya kai miliyan 3 da dubu 650, wanda ya karu da kashi 15 cikin dari, kana yawan kamfanonin dake hedkwata ko suka bude rassansu a yankin Hong Kong ya karu zuwa kimanin dubu 4, wanda ya karu da kashi 57 cikin dari.

Bisa jerin sunayen cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da aka fitar a watan Maris na bana, yankin Hong Kong ya ci gaba da cike matsayi na uku a duniya kana na farko a nahiyar Asiya, wannan ya sake tabbatar da matsayinsa na zama a kan gaba a fannin hada-hadar kudi a duniya. Ban da wannan kuma, bisa sabbin bayanai sun nuna cewa, yanayin cinikayya a yankin Hong Kong ya samu kyautatuwa, kana tattalin arzikin yankin yana bunkasa cikin sauri.

A karshen shekarar bara, yankin Hong Kong ya zama yanki mafi ingancin  tattalin arziki a duniya cikin shekaru 26 a jere. Masana tattalin arzikin yankin Hong Kong sun yi nuni da cewa, yankin ya samu wadannan nasarori ne, bisa goyon bayan Sin da kuma aiwatar da manufar “kasa daya amma tsarin mulki iri biyu”. Tun daga shekarar 1997 wato lokacin da yankin Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin, yankin ya samu babban ci gaba a matsayin cibiyar hada-hadar kudi ta duniya. (Zainab)