logo

HAUSA

Kwamitin raya kasuwanci da kungiyar ‘yan kasuwan kasa da kasa na kasar Sin duk suna adawa da shirin dokar wai magance aikin tilas ta Uygur

2022-06-29 21:36:12 CMG Hausa

Kwamitin sa kaimi ga ci gaban harkokin kasuwanci na kasa da kasa na kasar Sin, ya kira taron manema labarai a yau Laraba, inda kakakinsa Feng Yaoxiang ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka ta kirkiro batun “aikin tilas” a jihar Xinjiang ta kasar Sin, wanda ba shi da kanshin gaskiya ko kadan, al’amarin da ya keta hakkin dan Adam a jihar, da lalata muradun kamfanonin kasar Sin, kana yana kawo barazana ga aikin samar da kayayyaki a masana’antun duniya.

Kwamitin sa kaimi ga ci gaban harkokin kasuwanci na kasa da kasa na kasar Sin, gami da dukkan sassan kasuwancin kasar, za su yi kokarin samar da taimako a fannin doka ga kamfanonin da aka yiwa illa. (Murtala Zhang)