logo

HAUSA

Xi ya ziyarci Wuhan, inda ya jaddada aniyar Sin da dogaro da kanta ta fannin kimiyya da fasaha

2022-06-29 15:24:17 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada aniyar kasarsa na cigaba da tallafawa fannin kimiyya da fasaha bisa ikon da kasar ke da shi a kashin kanta, tare da bayyana aniyar kasar Sin na kara bunkasa cigban kasa ta hanyar dogaro da kanta, da tsayawa da kafafunta, da kuma kiyaye tsaron ci gaban kasar.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, kana shugaban hukumar koli ta sojojin kasar, ya yi wannan tsokaci ne a jiya Talata a lokacin da ya kai ziyarar aiki zuwa Wuhan, babban birnin lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin. (Ahmad Fagam)