logo

HAUSA

Sin da wasu kasashe 90 sun gabatar da bayanai kan hakkokin tattalin arziki, zaman rayuwa da al’adu a taron hakkin dan adam na MDD

2022-06-28 14:07:43 CMG HAUSA

 

A ranar Litinin kasar Sin ta gabatar da sanarwar hadin gwiwa tare da wasu kasashen duniya 90 a taron kolin hakkin adam na MDD karo na 50, inda suka zayyana muhimmancin daga matsayi da bada kariya ga hakkokin dake shafar tattalin arziki, zamantakewa da kuma al’adu, da nufin magance rashin daidaito a kokarin neman farfadowa daga annobar COVID-19.

A yayin gabatar da sanarwar hadin gwiwar a taron, Chen Xu, babban wakilin kasar Sin a ofsihin MDD dake Geneva, ya bayyana cewa, sakamakon manyan kalubalolin dake shafar zamantakewa da tattalin arziki, annobar COVID-19 ta kara fito da girman matsalolin rashin daidaito a tsakanin kasashen duniya, kuma kasashen da ba su da sukuni sun fuskanci yanayi na mayar da su saniyar ware, inda suka gamu da mummunan tasirin annobar.

Ya ce karancin makamashi, da rashin abinci, sun kara haifar da manyan kalubaloli ga kokarin da ake na neman farfadowa. Ya kara da cewa, sakamakon karuwar matsalolin, da mummunan tasirinsu ga rayuwar dan adam, da bukatu, da mutunci, har yanzu annobar ba ta zo karshe ba.

Don haka, jakada Chen ya ce, saboda muhimmancin da hakkin bil adama ke da shi, akwai bukatar kwamitin sulhun MDD ya dauki muhimman matakai don taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin samar da dawwamamen ci gaba, da tabbatar da daidaito da kuma samun muhimman sauye-sauyen farfadowa daga annoba. (Ahmad)