logo

HAUSA

Xi Jinping ya amsa wasikar da aka rubuta masa don karfafa gwiwar manyan manoman hatsi

2022-06-28 13:44:41 CMG Hausa

Jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da Xu Congxiang, wani babban manomin hatsi a gundumar Taihe na lardin Anhui ya rubuta masa, inda ya mika gaisuwarsa ga mazauna kauyukan, tare da kara sa rai ga manyan manoman kasar.

A wasikar da ya rubuta, Xi Jinping ya ce, a cikin ‘yan shekarun nan, gwamnatin tsakiya ta bullo da wasu tsare-tsare da matakai, don tallafawa masu noman hatsi, da nufin ba su damar samun kudi da Karin moriya, da kyautata rayuwarsu. Ana kuma sa ran manyan manoman hatsin kasar, za su yi amfani da damar ayyukan noman hatsi da suke da ita, wajen yin aiki tare da ma amfani da fasahar noma ta zamani, wajen janyo kananan manoma su kara noman hatsi, tare da ba da gudummawa wajen samar da abinci ga kasa cikin hadin gwiwa.(Ibrahim)