logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga Amurka da ta dakatar da cudanya da Taiwan

2022-06-28 20:42:29 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kasar sa na yin kira ga Amurka, da ta yi biyayya ga manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da ma sanarwar nan 3 da sassan 2 suka amincewa, ta kuma dakatar da dukkanin wata musaya da yankin Taiwan,  .

Zhao Lijian, ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da yake amsa tambaya game da wata manufa da aka yiwa take da “Shirin Amurka da Taiwan na raya cinikayya a karni na 21”.

Jami’in ya ce Sin na matukar adawa da cudanyar yankin Taiwan da dukkanin kasashe masu huldar jakadanci da kasar, ciki har da gudanar da tattaunawa, ko cimma matsaya kan wata yarjejeniya mai nasaba da samun ‘yancin kai, ko wadda aka gina ta a matsayi na hukuma. Zhao Lijian ya ce wannan matsaya ce tabbatacciya kuma a bayyane.  (Saminu)