logo

HAUSA

Masana’antar sarrafa na’urorin hakar mai da iskar gas a cikin teku ta hanyar amfani da na’urori masu kwakwalwa ta fara gudanar da aiki a Sin

2022-06-27 13:58:34 CMG Hausa

 

Jiya ne, masana’antar sarrafa na’urorin hakar mai da iskar gas a cikin teku ta hanyar amfani da na’urori masu kwakwalwa ta fara gudanar da aiki a hukumance, kuma, wannan ita ce masana’anta irinta ta farko da aka kafa a fadin kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, an sami gagarumin ci gaba a fannin sarrafa na’urorin hakar mai da iskar gas a cikin teku ta hanyar amfani da na’urori masu kwakwalwa.

Gaba daya, fadin masana’antar ya kai muraba’in mita dubu 575, ciki har da manyan cibiyoyin na’urori masu kwakwalwa guda 3, da wuraren gyara guda 7, da kuma wuraren hada kayayyaki guda 8. Kana, bisa shirin da aka tsara, za a samar da na’urori da nauyinsu ya kai ton dubu 84 cikin ko wace shekara, an kuma kafa tashoshin jiragen ruwa iri-iri a masana’antar.

Ban da haka kuma, akwai na’urori masu kwakwalwa sama da guda 400 a cikin wannan masana’anta, wadanda suka taimaka matuka wajen gaggauta gudanar da ayyuka.

An kafa wannan masana’anta ce bisa hadin gwiwar injiniyoyi sama da 200, da manyan jami’o’i da hukumomin kasar Sin, inda aka yi amfani da sabbin fasahohi kimanin 10, da sabunta fasahohi da dama ta fuskar amfani da na’urorin hakar mai da iskar gas a cikin teku ta hanyar sadarwa, da kuma sarrafa kayayyaki ta hanyar amfani da na’urori masu kwakwalwa.

Haka kuma, wannan masana’anta za ta iya samar da kayayyakin da darajarsu ta kai dallar Amurka miliyan 600 a ko wace shekara. (Maryam)