logo

HAUSA

Kamfanin Sin dake Afghanistan ya samar da kayayyakin agaji ga yankin da girgizar kasa ta auka a kasar

2022-06-27 11:32:43 CMG Hausa

Kamfanin kera karfe na kasar Sin wato MCC dake kasar Afghanistan mai aikin hakar tagulla mai suna Mes Aynak, ya samar da kayayyakin agaji ga yankin da ya yi fama da bala’in girgizar kasa a kasar Afghanistan, a birnin Khost na jihar Khost dake gabashin kasar.

Kayayyakin da kamfanin ya samar sun hada da shinkafa, da garin alkama, man girki, shayi da sauransu. Shugaban hukumar kula da ayyukan jin kai ta jihar Khost ya godewa kamfanin na Sin bisa gudummawar da ya samar, inda ya ce, Sin ta samar da kayayyakin bukata ga jama’ar yankin da  bala’in girgizar kasa ta aukawa a wannan muhimmin lokaci. (Zainab)