logo

HAUSA

Bincike: Da dama na tunanin dimokuradiyyar Amurka ta zama abin kunya

2022-06-27 12:02:43 CMG Hausa

Wani sabon bincike da shafin intanet na “Salon” na kasar Amurka ya gudanar ya gano cewa, fiye da rabin Amurkawa suna tunanin dimokuradiyya ta zama abin kunya. Amma hakan na iya zama gaskiya ne kawai idan aka mika wuya.

Jama'a a Amurka sun fahimci cewa, tsarin dimokuradiyyarsu da al'ummarsu na cikin babbar matsala. Amma ba su yarda a kan wane ne ko mene ne ya haddasa matsalar ba, kuma ba su fahimci hakikanin gaskiyar lamari ba. Abu mafi muni shi ne, akwai wata alaka tsakanin rikicin dimokuradiyyar Amurka da sauran manyan matsalolin da kasar ke fuskanta, kuma hakan hadari ne da zai iya durkusar da kasar baki daya.

A yayin shirye-shiryen jawabinsa a gaban kwamitin majalisa na ranar 6 ga watan Janairu a ranar Alhamis din da ta gabata, alkali mai ritaya J. Michael Luttig, dan jam'iyyar Republican mai ra'ayin mazan jiya, wanda ya shawarci tsohon mataimakin shugaban kasar Mike Pence kafin da kuma lokacin yunkurin juyin mulkin da Donald Trump ya yi, ya ba da wannan mummunan gargadi.

Yana mai cewa, an yi kokarin ruguza tsarin dimokuradiyyar Amurka a ranar 6 ga Janairun shekarar 2021, kuma dimokuradiyyarmu a yau tana kn siradi. (Ibrahim)