logo

HAUSA

Wakilan yankin Hong Kong na kasar Sin sun bayyana halin da ake ciki a yankin a wajen taron UNHRC

2022-06-26 17:53:55 CMG Hausa

Kwanan nan, wakilai biyu daga yankin Hong Kong na kasar Sin, wato Dr. Edmund Ng da Kevin Lau Chung-hang, sun gabatar da jawabai game da halin da Hong Kong take ciki a wajen taro karo na 50 na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ko kuma UNHRC a takaice. 

Dr. Edmund Ng, wani malamin addinin Kiristanci ne wanda ya nuna cewa, a shekaru 25 da suka shude, muhimmiyar manufar da ake kira “kasancewar kasa daya amma tsarin mulki biyu” ta samar da tabbaci ga ‘yancin bin addinai da neman ilimi a Hong Kong. Kana, bayan da aka aiwatar da dokar tsaron kasa a yankin, an kara samun tabbacin ‘yanci a wadannan fannonin. Malaman addinai a Hong Kong za su ci gaba da bayar da gudummawa wajen raya wurin.

A nasa bangaren kuma, wakilin matasan Hong Kong, Kevin Lau Chung-hang ya ce, ana dab da bikin murnar cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong kasar Sin. Dokar tsaron kasa gami da sabon tsarin gudanar da zabe sun kiyaye hakkokin mazauna gami da kamfanonin Hong Kong, al’amarin da ya maida yankin turbar samun bunkasuwa da shugabanci nagari. Karkashin goyon-baya da taimakon gwamnatin kasar Sin, Hong Kong da jama’arta suna da yakinin kara samun ci gaba.

Kevin Lau ya kara da cewa, babu wani salon demokuradiyya wanda ke dacewa da kowace kasa a duniyarmu, ita Amurka wadda take ikirarin cewa wai kasa ce mafi dogon tarihi wajen tabbatar da tsarin demokuradiyya a duniya, tana yunkurin tada yakin kasuwanci da keta dokokin kasa da kasa, maimakon ta shawo kan matsalolin kanta, ciki har da hauhawar farashin kaya mai tsanani da yawan harbe-harben da ake yiwa yaran makarantu. Wannan sam ba ita ne demokuradiyyar da ake bukata ba. (Murtala Zhang)