logo

HAUSA

WHO: Barkewar cutar kyandar biri a kasashe da dama bai mayar da cutar zuwa mataki mafi hadari ga lafiyar al’umma ba

2022-06-26 17:26:39 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar a yau Lahadi cewa, barkewar cutar kyandar biri wato monkeypox, da ta yadu a kasashen duniya sama da 50 a baya bayan nan, bai nuna cewa cutar ta kai matakin mafi hadari ga lafiyar al’ummar kasa da kasa ba.

Sai dai kuma, bisa lura da yanayin hadarin kara yaduwar cutar a sassan duniya, bai kamata a kawar da kai daga batun cutar ba, kamar yadda wasu daga cikin mambobin kwamitin gaggawa na hukumar WHO suka bayyana a rahoton barkewar cutar, bayan kammala taronsu a ranar Alhamis.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, an nuna rashin kulawa game da batun cutar kyandar biri, kuma ba a dauki matakan dakile cutar ba a shekaru da dama a kasashen da ke karkashin kulawar hukumar WHO reshen  shiyyar Afrika.

Babban daraktan hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bukaci a dauki matakan sanya ido, da inganta binciken yanayin masu fama da cutar, da shigar da al’umma cikin shirin wayar da kai game da hadarin cutar, da musayar bayanai kan cutar, da kuma bin hanyoyi mafi dacewa na magance cutar, da samar da riga-kafi da sauran matakan kare lafiyar al’umma.

Ya kuma bukaci kasashen duniya su hada kai, da yin musayar bayanai, kana da hada gwiwa da al’ummomin yankunan da cutar ta bulla, domin a samu damar daukar matakan kariya cikin gaggawa da kuma nasarar kawar da cutar yadda ya kamata.

An samu rahoton adadi mai yawa na barkewar cutar monkeypox a ‘yan makonnin da suka gabata a kasashen duniya da dama, da suka hada da yankin Turai, da arewacin Amurka, shiyyoyin da ba safai ake samun bullar cutar ba.(Ahmad)