logo

HAUSA

Mataimakin shugaban NDB: Ya dace a tsaya ga ra’ayin cudanyar bangarori daban daban

2022-06-25 16:11:07 CMG Hausa

Mataimakin shugaban sabon bankin raya kasashen BRICS wato NDB Zhou Qiangwu, ya bayyana cewa, sabon bankin zai kara habaka aikinsa a fadin duniya. Kuma ya dace kasashen duniya su tsaya ga ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, ta yadda za su yi hadin gwiwa na hakika, tare kuma da daidaita matsalolin da suke fuskanta.

Zhou Qiangwu, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labaran babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a jiya.

Jami’in ya kara da cewa, kawo yanzu, bankin ya riga ya amince da ayyukan ba da rancen kudi sama da 80 wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 30, domin goyon bayan ci gaban kasashe mambobin kungiyar a bangarorin samar da makamashi mai tsabta, da sufuri, da gina birane, da samar da ruwa mai tsabta, da gina kayayyakin more rayuwar jama’a da sauransu. (Jamila)