logo

HAUSA

MDD ta bukaci a sake shigar da kayayyakin abinci da Ukraine da Rasha ke samarwa cikin kasuwannin duniya

2022-06-25 16:02:26 CMG Hausa

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya jaddada muhimmancin sake shigar da kayayyakin abinci da taki da kasashen Ukraine da Rasha ke samarwa cikin kasuwannin duniya.

Cikin wani sakon bidiyo da ya aika jiya, ga taron ministoci kan wadatar abinci a duniya da aka yi a birnin Berlin na Jamus, Antonio Guterres, ya yi gargadin cewa za a iya samun matsalolin yunwa da dama a shekarar 2022, wadanda ka iya tabarbarewa a shekarar 2023.

Ya ce abubuwa masu tsada ga manoma su ne taki da makamashi. Ya ce farashin taki ya tashi da sama da rabi cikin shekara guda, haka kuma an samu karuwar farashin makasahi da sama da kaso biyu cikin uku. Lamarin da ya ce, zai shafi girbi, ciki har da na masara da shinkafa, tare da shafar biliyoyin mutane a fadin nahiyoyin Asia da Afrika da Amurka. Ya kara da cewa, matsalolin samun abinci da ake fama da su a bana, ka iya zama matsalar karancin abinci a duniya a badi. Kuma babu wata kasa da ke da kariya daga mummunan tasirin matsalar kan tattalin arziki da zamantakewa.

Ya ce matsalar ta zarce batun abinci kadai, don haka akwai bukatar daukar dabaru daban daban da za su samar da mabambantan mafita.  (Fa’iza Mustapha)