logo

HAUSA

Wang Yi ya yi tsokaci kan nasarori goma da BRICS ta samu a bana

2022-06-25 15:49:59 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce hadin gwiwar dake tsakanin kasashen kungiyar BRICS ya kai matsayin koli, inda aka samu muhimman nasarori 10 a bangarori daban daban.

Wang Yi ya bayyana haka ne jiya, yayin zantawa da menama labaran manyan kafofin watsa labarai na kasar, game da ganawar shugabannin kasashen kungiyar BRICS karkashin jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping, da taron tattauna ci gaban kasa da kasa.

A cewarsa, an samu manyan sakamakon da yawansu ya kai 37 a bana, kana nasarorin goma da kasashen suka samu sun hada da: nacewa kan tabbatar da adalci tsakanin kasa da kasa ta hanyar fitar da “sanarwar Beijing”, da inganta aikin dakile annobar cutar COVID-19 ta hanyar kafa “cibiyar nazarin allurar rigakafin cutar ta kasashen BRICS”, da ba da gudumowa ga ci gaban tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, da kara karfafa aikin yaki da cin hanci da rashawa, da kafa babbar kasuwar da ta dinke kasashen BRICS, da kokarin tabbatar da aikin samar da isasshen abinci ga al’ummomin kasa da kasa, da amfani da boyayyen karfin kirkire-kirkire domin samun ci gaba tare, da kara habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen mambobin kungiyar a bangaren kimiyya da fasaha ta zamani, da amfani da damammakin raya tattalin arziki ta yanar gizo a sabon zamanin da ake ciki, da kuma horas da masana fasahohi, ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa a nan gaba. (Jamila)