logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya jaddada bukatar samar da tsarin adana bayanai da tafiyar da harkokin shugabanci

2022-06-25 15:34:52 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma shugaban hukumar koli ta zurfafa gyare-gyare a kasar, ya jagoranci taron hukumar karo na 26 da ya gudana ranar Laraba, inda aka yi bita tare da amincewa da wasu ka’idoji da shirye-shirye.

Daga cikinsu, akwai ka’idojin samar da tsarin adana bayanai da kyautata amfani da hanyoyin samar da bayanai da ka’idojin inganta ayyukan da suka shafi sassan kula da harkokin mulki da shirin kan gwajin gyara aikin tantance jami’ai masana kimiyya da fasaha da aiwatar da shirin inganta sa ido kan manyan dandamalin biyan kudi da ingantawa tare da samar da fasahohin hada-hadar kudi. (Fa’iza)