logo

HAUSA

Asunsun IMF na ganin babu hanyoyin masu yawa na kaucewa durkushewar tattalin arziki a Amurka

2022-06-25 16:37:45 CMG Hausa

Shugabar asusun bada lamuni na duniya, Kristalina Geogieva, ta ce asunsun IMF na ganin babu hanyoyin masu yawa na kaucewa durkushewar tattalin arzikin Amurka, ta na mai bayyana mummunan tasirin da hakan zai haifar.

Ta ce bisa manufofin da kwamitin kula da harkokin kasuwanci na Amurka ya gabatar yayin taronsa na wannan wata, da yuwuwar raguwar gibin kasafin kudi, suna sa ran tattalin arzikin Amurka zai yi tafiyar hawainiya.

Kristalina Georgieva, ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai game da sakamakon nazarin tattalin arzikin Amurka na bana dake karkashin aya ta 4 ta yarjejeniyar asusun da Amurka.

A cewarta, asusun IMF ya yi ammana cewa, adadin kudin ruwa da babban bankin kasar ya bayyana, domin gaggauta kai shi tsakanin kaso 3.5 zuwa 4, ita ce manufar da ta dace da rage hauhawar farashi a kasar.

Ta kara da cewa, sun damu, bisa la’akari da cewa, hanyar kaucewa durkushewaer tattalin arzikin Amurka bata da yawa. Haka zalika, sun damu da rashin tabbacin dake tattare da yanayin. (Fa’iza)