logo

HAUSA

Wang Yi ya aike da sakon jaje game da girgizar kasar da ta aukawa Afghanistan

2022-06-25 19:42:55 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya aike da sakon jaje ga Amir Khan Muttaqi, mukaddashin ministan harkokin wajen gwamnatin riko na Aghanistan, dangane da girgizar kasar da ta aukawa kasar.

A cewar Wang Yi, a matsayin makwabciya kuma abokiya, a shirye Sin take ta yi iyakar kokarinta na samar da taimakon gaggawa da za su dace da bukatun kasar Afghanistan. (Fa’iza Mustapha)