logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga Amurka da kasashen yamma su soke takunkuman da suka yi gaban kansu wajen kakabawa

2022-06-25 16:20:01 CMG Hausa

Kasar Sin, ta yi kira ga Amurka da kasashen yammacin duniya, su gaggauta soke takunkuman da suka yi gaban kansu wajen kakabawa, da dakatar da keta hakkokin jama’a a wasu kasashe.

Wakilin na Sin ne ya yi kiran a jiya, yayin zama na 50 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, a lokacin da yake halartar tattaunawar da aka yi tsakanin wasu masana masu zaman kansu, a bangren hakkokin bil adama da hadin giwar kasashen duniya. (Fa’iza)