Jakadan Sin ya gana da tsohon shugaban kasar Nijer
2022-06-24 11:03:11 CMG HAUSA
A ranar 23 ga watan Yuni, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Nijer Jiang Feng ya gana da tsohon shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou. Bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi game da kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma yanayin da ake ciki a yankin Sahel.
Ambasada Jiang ya gabatar da jawabi game da yanayin ci gaban da aka samu a manyan ayyukan hadin gwiwar Sin da Nijer tare da bayyana fatar Issoufou zai cigaba da nuna goyon baya game da hakikanin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijer. Jiang ya kuma taya Muhammadu Issoufou murnar zama jami’i mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS game da batun dake shafar kasar Burkina Faso, sannan ya bayyana cewa kasar Sin a shirye take ta karfafa tuntubar juna, da kuma yin aiki tare da ECOWAS, kana da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Sahel.
A nasa bangaren, Issoufou ya yi bayani game da abokantakar dake tsakanin Sin da Nijer, sannan ya bayyana nasarorin da aka cimma karkashin kyakkyawar huldar dake tsakanin kasashen biyu, kana ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da ba da gudunmawa wajen zurfafa kyakkyawar hulda da hadin gwiwar bangarorin biyu. Ya ce yanayin da ake ciki a halin yanzu a yankin Sahel abin damuwa ne. Don haka yana fatan dukkan bangarori, ciki har da kasar Sin, za su ci gaba da nuna goyon baya ga shiyyar, kana za su taimakawa kasashen dake shiyyar domin kawo karshen wahalhalun da ake fuskanta. (Ahmad Fagam)