logo

HAUSA

Za a fara watsa shirye-shiryen talibijin da na rediyo na CMG a Hong Kong

2022-06-24 16:24:40 CMG Hausa

 

Yau Jumma'a 24 ga wata, aka yi bikin kaddamar da watsa shirye-shiryen talibijin na tashar Documentary ta CGTN da shirye-shiryen rediyo na tashar The Greater Bay na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG a Beijing da Hong Kong a sa’i guda. Inda aka sanar da cewa, za a fara watsa shirye-shiryen CMG a Hong Kong kai tsaye a ranar 1 ga wata mai zuwa, a matsayin wata kyauta ta murnar cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong karkashin mulkin kasar Sin, da kuma wani mataki na taimaka wa gudanar da manufar “kasar Sin, mai tsarin mulki biyu” a Hong Kong yadda ya kamata. (Kande Gao)