logo

HAUSA

Xi: Sin za ta dauki managartan matakai don ci gaba da tallafawa ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan da 2030

2022-06-24 20:58:12 CMG Hausa

A yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci wani babban taron tattaunawa kan ci gaban duniya ta kafar bidiyo, tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, sai al'ummomin kasashen duniya suna rayuwa mai kyau ne kadai za a iya samun dorewar wadata, da tabbatar da tsaro, da kare hakkin dan-Adam. Kasar Sin za ta dauki managartan matakai, don ci gaba da tallafawa ajandar samun dauwamammen ci gaba ta MDD nan da shekarar 2030. Kasar Sin za ta kara zuba jari a fannin samar da albarkatu a hadin gwiwar raya kasa da kasa, da yin hadin gwiwa da dukkan bangarori, don inganta hadin gwiwa a muhimman fannoni: zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen rage fatara da kawar da talauci, da inganta samar da abinci da hanyoyin samar da kayayyaki, da inganta hadin gwiwar makamashi mai tsafta, karfafa yin bincike da samar da alluran rigakafi cikin hadin gwiwa, inganta hadin kai a fannin sabbin fasahohi zamani, ya haifar da sabon kuzari ga ci gaban kasashe baki daya. (Ibrahim)