logo

HAUSA

Babban sakataren MDD ya yi kira da a tallafawa al’ummar Afghanistan da girgizar kasa ta rutsa da su

2022-06-23 11:49:10 CMG HAUSA

 

António Guterres, babban sakataren MDD ya nuna bakin ciki matuka kan hasarar rayukan mutane da yawa da kuma jikkatar wasu a girgizar kasar a gabashin kasar Afghanistan a ranar 22 ga wata, tare da yin kira ga kasashen duniya da su taimakawa al’ummar Afghanistan wadanda bala’in ya rutsa da su.

Guterres ya bayyana haka ne cikin wata sanarwar da ya bayar jiya Laraba, ya kara da cewa, hukumomin MDD da ke Afghanistan sun zage damtse wajen kimanta bukatun da ake da su ta fuskar taimakon jin kai da bayar da taimako. Babban jami’in MDD ya yi kira ga kasa da kasa da su ba wa al’ummar Afghanistan da bala’in ya shafa taimako.

A ranar 22 ga wata da sanyin safiya ne aka yi mummunar girgizar kasa a gabashin kasar Afghanistan, wadda ta fi yin barna a lardin Khost da na Paktika da ke gabashin kasar. Wani jami’in wurin ya gaya wa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin cewa, girgizar kasar da zabtarewar kasa da ta abku biyo bayan girgizar kasar sun haddasa mutuwar mutane a kalla 1000, tare da jikkata 1500. Wannan shi ne girgizar kasa mafi muni da ta fi haddasa mutuwar mutane a kasar ta Afghanistan cikin shekaru 20 da suka gabata. (Tasallah Yuan)