logo

HAUSA

Xi: Ya kamata kasashen BRICS su shigar da dabaru masu nagarta a duniya

2022-06-23 20:45:17 CMG Hausa

A yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron shugabannin BRICS karo na 14 da ya gudana ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi Jinping ya jaddada cewa, wannan taron na cikin wani muhimmin lokaci game da inda daukacin al’umma suka dosa. A matsayinmu na muhimman kasashe da tattalin arzikinmu ke saurin bunkasa da kuma manyan kasashe masu tasowa, tilas ne kasashen BRICS su kasance masu jajircewa, wajen sauke nauyin dake bisa wuyansu da aikace, tare da shigar da matakan da suka dace a duniya. Na farko, wajibi ne mu yi magana da murya ta gaskiya da adalci. Na biyu, tilas ne mu yi imani da gaske wajen magance annoba. Na uku, dole ne mu karfafa hadin gwiwar farfado da tattalin arziki. Na hudu kuma, dole ne mu yayata ci gaba mai dorewa. (Ibrahim)