logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci a dage takunkumin hana sayar da makamai ga CAR

2022-06-23 13:44:58 CMG HAUSA

 


Jakadan kasar Sin ya yi kira ga kwamitin sulhun MDD da a janye takunkuman hana sayar da makamai ga jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, ba tare da bata lokaci ba.

Ministan harkokin wajen CAR ya rubuta wasika ga shugaban kwamitin sulhun MDD a ranar 8 ga watan Yuni, inda ya bayyana cewar takunkuman hana sayar da makaman yana haifar da mummunan tasiri ga shirin tsaron jamhuriyar tsakiyar Afrika, kana ya jaddada kokarin da gwamnatin CAR ke yi wajen aiwatar da kudurorin kwamitin sulhun MDD, da yadda za a tabbatar janyewa kasar takunkuman hana sayen makamai.

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce kasar Sin tana fatan kwamitin sulhun zai saurari bukatun da CAR ta nema, kana za a dage mata takunkuman a kan lokaci, domin taimakawa jamhuriyar tsakiyar Afrikan wajen shawo kan kalubalolin tsaro, da kuma samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Ya yi kira ga kasa da kasa, da su tallafawa CAR don farfadowar tattalin arzikinta, da kuma rage wahalhalun da ake fuskanta game da yanayin ayyukan jinkai a kasar.

Ya ce akwai bukatar a kara zuba jari wajen samar da abinci, da gina kayayyakin more rayuwa, da inganta ilmi, da kiwon lafiya, da horar da sana’o’i, da sauran fannonin da za su taimaka wajen kawar da talauci a CAR, da kuma kyautata zaman rayuwar al’ummar kasar, da yin amfani da makamashin da kasar ke da su wajen raya ci gaban kasa domin a cimma nasarar kawar da matsalolin tashe-tashen hankula tun daga tushe. (Ahmad)