logo

HAUSA

Kamfanin Sin ya hada gwiwa da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD don bayar da ilmi ga matasa ‘yan gudun hijira a Afrika

2022-06-22 13:33:01 CMG HAUSA

 

Kawar da cikas wajen samun ilmi mai inganci ga ‘yan gudun hijira da ingiza su shiga kasuwar kwadago, mataki ne dake da muhimmanci sosai ga aikin ba da ilmi ga ‘yan gudun hijira dake Afrika. A ran 20 ga wata, kamfanin TECNO na birnin Shenshen na kasar Sin ya sanar da baiwa hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD wato UNHCR kyautar kudin karatu.

Wakilin UNHCR dake Sin Vanno Noupech ya bayyana godiyarsa ga kamfanin TECNO yana cewa, hukumar na maraba da bangarorin biyu su habaka hadin gwiwarsu, wanda zai taka rawa wajen taimakawa ‘yan gudun hijirar dake cikin mawuyancin hali, su shiga kasuwar kwadago.

Babban directan kamfanin TECNO Zhu Zhaojiang ya bayyana cewa, TECNO na fatan habaka taimako da daga matsayin ba da ilmi da yake baiwa dalibai ‘yan gudun hijira ta hanyar sake hada gwiwa da UNHCR. Ya ce tsarin samar da kyautar kudin karatu ga ‘yan gudun hijira dama ce da zata taimakawa wasu matasa dake da boyayyen karfi da buri wajen ci gaba da samun ilmi, ta yadda za su kyautata zaman rayuwarsu da amfanawa al’ummar Afrika. Bugu da kari, ban da samar da kyautar kudin karatu, kamfanin zai samar da damar horon aiki da guraben aikin yi ga matasan Afirka masu gudun hijira. (Amina Xu)