Kasancewar Mutane Masu Akidu Da Al’adu Daban-Daban Na Bukatar Hakuri Da Mutunta Juna
2022-06-21 18:15:15 CMG Hausa
Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da wani taro a jiya, albarkacin ranar adawa da kalaman kiyayya ta duniya, inda zaunannen wakilin Sin dake majalisar Zhang Jun ya yi kira ga kasashen duniya su mutunta tare da hakuri da juna, kana su rika tattaunawa cikin adalci don yaki da kalaman kiyayya. Kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka gabatar da kudurin ayyana ranar ta yaki da kalaman kiyayya a shekarar 2021, inda aka fara gudanar da ita karon farko a bana.
Kamar yadda wakilin na Sin ya bayyana, yaki da kalaman kiyayya na bukatar kasashe su mutunta ’yanci da moriyar juna, da watsi da girman kai. Matukar da gaske ana son cimma zaman lafiya a duniya, to ya kamata gwamnati ta zama abar koyi ga jama’arta. Bai dace gwamnati ta rika yada karairayi da zarge-zarge ba, domin jama’arta za su yi koyi da ita, lamarin da zai haifar da gadon kiyayya mara tushe tsakanin al’ummomi. Misali, an ga yadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya rika danganta annobar COVID-19 da kasar Sin, lamarin da ya sa aka rika nuna kyama ga mutanen Sin da Asiya a kasar da sauran kasashen yamma. Ko a lokacin babban zaben kasar, irin furucinsa ne ya haifar da harin da magoya bayansa suka kai ginin majalisa ta Capitol a kasar.
Hakuri shi ne tushen zaman lafiya. Kasancewar mutane daban-daban, masu addinai da akidu da launi da al’adu daban-daban, na bukatar hakuri da mutunta juna. Hadin kan kasa da kasa don moriyar juna, cikin adalci da mutunta juna, zai iya tabbatar da zaman lafiyar da ake muradi. Haka zalika shirye-shirye kamar irin na abota tsakanin matasan Sin da Afrika dake zaman dandalin musaya, zai yi gagarumin tasiri wajen kawar da rashin fahimtar dake haifar da kiyayya. A ganina, nan gaba, matasan Sin da Afrika da za su zama manyan gobe, za su kasance tamkar ’yan uwa ba tare da la’akari da bamban-bambacen dake tsakaninsu ba. Irin wannan shiri da makamantansa, za su kawar da kyama da kiyayya don tabbatar da zaman lafiya da mutunci da kuma jituwa tsakanin al’ummomi. Wannan, shiri ne da ya kamata sauran kasashe su yi koyi da shi yayin da ake kokarin kawar da kiyayya a duniya. (Fa’iza Muhammad Mustapha)