logo

HAUSA

Takardar da ta tona karairayin Amurka

2022-06-21 11:44:31 CMG Hausa

A karshen watan Mayun da ya gabata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya gabatar da wani jawabi a kan manufofin kasar Amurka a kan kasar Sin, inda ya sha tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da ma shafa wa kasar bakin fenti a kan manufofinta na gida da waje. Sai dai kome kokarinta, ba ta iya boye ainihin burin da take neman cimmawa na dakile ci gaban kasar Sin daga dukkan fannoni ba. A ranar 19 ga wata da dare, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata takarda mai taken "Kura-kurai da ke tattare da ra'ayin Amurka game da kasar Sin da ma ainihin gaskiyar abubuwan", inda ta fallasa "yadda yaudara, munafunci da hadarin dake kunshe cikin manufofin Amurka game da kasar Sin" tare da cikakkun bayanai da kuma alkaluma.

Wace ce ke lalata tsarin kasa da kasa? Wace ce kuma ke keta hakkin dan Adam a sassan duniya da ma satar sauraron kusoshin kasa da kasa? Wannan takarda mai kunshe da dogon bayani ta zayyano kura-kurai da ma karairayi kimanin 21 da ke tattare da manufofin kasar Amurka a kan kasar Sin, ta kuma samar da cikakkun bayanai da alkaluma don fadakar da kasashen duniya a kan yadda kasar Amurka ke haifar da rikici ga duniya, da kuma tilastawa wasu kasashe su bi tsarinta a harkokin diplomasiyya, da ma yadda ta fi kowace kasa a duniya wajen lalata hakkin dan Adam da kuma kai hare-hare ta yanar gizo.

Daga cikinsu kuwa, furucin ’yan siyasar Amurka dake cewa wai “Sin na haifar da kalubale mafi tsanani ga tsarin kasa da kasa” na daga cikin munanan karairayi da suka yi, kuma abin dariya ne yadda suka furta cewa, wai “Amurka na kare dokoki da yarjejeniyoyi da ka’idoji da ma hukumomi na kasa da kasa.” Ban da haka kuma, kasar Amurka tana kuma kokarin kafa “tsarin tattalin arzikin Indo-Pasifik”, a yunkurin kafa tsarin ka’idojin ciniki da ke karkashin jagorancinta, tare da tilasta kasashen shiyyar da su katse huldar ciniki da kasar Sin. Tsarin wanda ke kare moriyar Amurka, ya kuma haddasa cikas ga farfadowar tattalin arzikin duniya bayan annoba. Kome kokarinta, Amurkar ba za ta iya boye burin da take neman cimmawa na dakile ci gaban kasar Sin da kuma neman shimfida tsarin yin babakere a duniya. (Lubabatu)